Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Hussain Salami yana fadar haka a yau Alhamis a lokacinda ya kai ziyara dandalin baje kolin kayakin yaki na lantarki da jiragen yakin da ake sarrafa su daga Nesa a nan birnin Tehran.
Salami ya kuma kara da cewa kasar Iran a shirye take take fuskanci duk wata barazanar tsaro wanda kasar zata fuskanta a ko wani lokaci. Ya kuma kara da cewa kamfanonin kera makaman kasar sun sami ci gaba sosai ta yadda suka iya kera makamai wadanda suke tafiya da zamani sannan da kuma fuskantar makiya a kan duk wata Gadara da suke tunanin suke da shi.
Daga karshe Janar Salami ya bukaci kamfanonin kare makamai a kasar su ci gaba da kokarin ganin sun rage tazara tsakanin kasar da Iran da sauran kasashen da suka ci gaba a bangaren makaman zamani.
342/